A wajen taron da ya gudana a kwanakin baya, an jefa kuri'a don tabbatar da nada mista Leung Chun Ying, shugaban yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin, a matsayin mataimakin shugaban majalisar CPPCC ta kasar Sin, gami da zartas da jerin dokoki.
A jawabinsa yayin rufe taron, shugaban majalisar CPPCC ta kasar Sin, mista Yu Zhengsheng, ya bayyana cewa, 'yan majalisar na matukar alfahari saboda babban nauyi dake wuyansu. Don haka kamata ya yi su yi kokarin sauke wannan nauyi yadda ya kamata, da ba da nagartatun shawarwari kan harkokin siyasa na kasar, don taimakawa gwamnatin kasar aiwatar da manufofinta, da kara samar da alheri ga jama'ar kasar. Hakan, a cewar shugaban majalisar, sun kasance manyan ayyukan da ya kamata a kula da su, a wannan lokaci mai muhimmanci da muke ciki. (Bello Wang)