A ranar Litinin ne dai wasu kafofin watsa labarai na Afirka ta kudu, suka fidda wasu rahotanni, dake cewa kamfanin ya koka, bayan da ya gano matsaloli tattare da jiragen da ya sayo daga kasar Sin. Kuma wai Transnet din ya ki amincewa ya karbi karin wasu jiragen 18 da ya yi odar su daga Sin.
Sabanin hakan, kamfanin ya ce a shekarar 2014, ya sanya odar kawunan jiragen kasa har 1,064 daga wasu kamfanonin Sin 4.
Da yake karin haske game da wannan batu, babban manajan kamfanin sashen labarai Molatwane Likhethe, ya ce jita jitar da wasu kafofin watsa labarai ke yadawa ba ta da tushe bare makama.
Mr. Likhethe ya ce kamfanin CRRC na Sin, ya riga ya mika kawunan jiragen kasa 2 da ya kera domin a gwada su a Afirka ta kudu, kafin kammala sauran odar ta sa.
Dama dai tun da fari, an shirya cewa CRRC zai kera kawunan jiragen kasa 20 na farko a Sin, sa'an nan ya hada sauran a sashen kere kere na kamfanin Transnet dake birnin Durban. Kaza lika kuma, za a tabbatar da cewa 18 na wadannan jirage da za a kera su a Sin, an yi musu cikakken gwaji kafin a kai su Afirka ta kudun.