Babban jojin kasar Sin Zhou Qiang, wanda ya bayyana haka yayin da yake gabatar da rahoton bangaren shari'a ga taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin NPC, ya ce daga cikin wadanda aka tuhuma yayin shari'un sun har da da tsoffin ministoci da jami'ai a matakin larduna guda 35 da wasu 240 a matakin yankuna .
Tun lokacin babban taron wakilan Jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin a shekarar 2012 ne kasar Sin ta kaddamar da gagarumin yaki da cin hanci da rashawa, inda a karshen shekarar da ta gabata ne shugabancin jam'iyyar ta sanar da cewa shirin ya samu dimbin nasarori.
A cewar rahoton da mai gabatar da kararraki a kotu na kasar Sin ya gabatar, a cikin shekarar 2016, hukumomin gabatar da kararraki sun gudanar da bincike kan mutane 47,650 da ake zargi da aikata laifuka da suka danganci gudanar da ayyukansu.
hukumomin sun kuma gudanar da bincike kan wasu kananan jami'ai 17, 410 da ake zargi da aikata cin hanci a fannonin daban-daban da suka shafi kyautata rayuwar al'umma. ( Fa'iza Mustapha)