in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kotun koli ta kasar Sin ta ce 'yan tsirarrun shari'u da masu tsananin laifuka ne kadai ake yankewa hukuncin kisa
2017-03-12 12:30:32 cri
Kotun koli na jam'ar kasar Sin, ta ce 'yan tsirarun shari'un da laifukansu suka yi kamari ne kadai, kotunan kasar suka yankewa hukuncin kisa a cikin shekaru goma da suka gabata.

Da yake gabatar da rahoton bangaren shari'a ga taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin dake gudana, babban jojin kasar Zhou Qiang ya ce, tun a shekarar 2007, da kotun kolin ta zartar da cewa sai ta sake nazarin duk hukuncin kisa da kananan kotuna suka yanke, ba a yanke huncin kisa sai an tsallake duk wasu ka'idoji an kuma bi diddigin laifi. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China