Sanarwar ta bayyana cewa, ana zarginsu da aikata laifuffukan janyo barazana ga gwamnatin kasar Habasha, ciki har da tsara da tada rikici, lalata gine ginen gwamnati, raunata fararen hula da jami'an tsaron kasar da dai sauransu.
A kwanakin baya, an yi rikici a tsakanin 'yan kabilar Oromo dake yankin Oromia na kasar da gwamnatin kasar kan batun mayar da filaye a hannun gwamnati, lamarin da ya janyo zanga-zanga a yankin, da tayar da rikici tsakanin mazauna wurin da 'yan sanda, wanda ya haddasa mutuwar mutane da dama, da tsananta halin da ake ciki a yankin.
A ranar 9 ga watan Oktoba, gwamnatin kasar Habasha ta sanar da ayyana dokar-ta-bace har na tsawon watanni 6 a kasar don tabbatar da kwantar da hankali. Ban da wannan kuma, an kyautata membobin gwamnatin kasar, da kara yawan kujeru ga 'yan kabilar Oromo domin kwantar da damuwar 'yan kabilar Oromo din. (Zainab)