Mr. Oqubay wanda ya shaida hakan ga kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua, ya kara da cewa aikin zai kuma fadada cin gajiyar kasashen biyu a bangaren musayar fasahohin sufuri na zamani. Kaza lika zai bunkasa harkokin shige da ficen hajoji da inganta ci gaban masana'antu a kasar ta Habasha.
Jami'in ya ce baya ga wadannan manyan damammaki da kasar za ta samu, sabon layin dogon zai kuma karfafa kawance, da hadin gwiwa dake tsakanin Habasha da kasar Sin.(Saminu Alhassan)