in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Habasha ta sanar da kafa dokar ta baci na watanni 6
2016-10-10 10:24:48 cri

Rahotanni daga kasar Habasha na cewa, a jiya ne firaministan kasar Hailemariam Dessalegn ya sanar da kafa dokar ta baci na watanni 6 a kasar, domin tinkarar tashe-tashen hankalin kasar da suka barke sakamakon zanga-zangar da mazauna yankin Oromia suka yi.

Hailemariam Dessalegn ya kara da cewa, a ranar Asabar majalisar ministocin kasar Habasha ta kira taron gaggawa game da halin da kasar ta shiga inda ta tsai da kudurin kafa dokar ta baci a kasar. Ya ce, an yanke wannan kuduri ne sabo da tabbatar da zaman lafiya a kasar da tsaron jama'a.

A kwanan baya ne, al'ummar yankin Oromia suka shirya zanga-zangar nuna adawa da gwamnati da neman 'yancin filaye da yadda gwamnati take rushe musu gidaje, lamarin ya kai ga yin arangama da sojoji da 'yan sanda. Hakan zanga-zangar ta yi sanadiyyar mutuwa da jikkatar mutane da dama, kuma yanayin ya ci gaba da tsananta.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China