Kungiyar masu tsattsauran ra'ayi na Jabhat Fateh al-Sham ta sanar da daukar alhakin kai harin.
Gwamnan jihar Homs Talal Barazi, ya bayyana wa 'yan jarida cewa, an kai harin ta'addancin ne domin mayar da martani ga sojojin gwamnatin kasar, dake samun nasara a fannin aikin soji a Homs da kuma nasarar da wakilan gwamnatin kasar suka samu yayin taron birnin Geneva.
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Syria ta bayyana cewa, 'yan ta'adda sun kai hare-hare a jere a birnin Homs na kasar Syria, don kawo cikas ga aiwatar da batutuwan da aka cimma a wajen taron tabbbatar da zaman lafiya a birnin Astana .
A ranar 23 ga wannan wata, an sake yin shawarwarin shimfida zaman lafiya kan batun Syria a birnin Genava da aka dakatar da su har na tsawon watanni 10.
Shugaban tawagar wakilan gwamnatin kasar Syria Bashar Ja'afari ya bayyana cewa, ya riga ya bukaci dukkan wakilan masu adawa su bayar da ra'ayoyinsu kan harin bom da aka kai a birnin Homs don tabbatar da cewa, su abokan yin shawarwari ne, ba abokan 'yan ta'addanci ba. (Zainab)