Wani rahoton da kungiyar 'yan kasuwa ta EU ta fidda kwanakin baya, ya yi suka ga shirin, inda ya ce mai yiyuwa ne ba zai dace da yanayin kasuwa a halin yanzu ba, sakamakon wasu matakan kariyar ciniki dake kunshe a cikinsa.
Da yake jawabi yau Asabar a birnin Beijing, Miao Wei ya mai da martini ga wannan rahoto, inda ya jaddada cewa, shirin bai kunshi wata matsala ta musamman ga kamfanonin kasashen ketare dake zaune a kasar Sin ba, balle ma ya matsa musu lambar samar da fasahohinsu ga kasar Sin.
Bugu da kari, ya ce, gwamnatin kasar Sin ta yi ta jaddada aniyarta, ta karfafa hadin gwiwa da mu'amala tsakaninta da kasashen ketare, a yayin da take inganta shirin kere-keren na Made in China 2025. (Maryam)