Mr Gao wanda ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a yau Talata, ya ce a shekarar 2016 da ta gabata kasar Sin ta kara bullo da wasu manufofin hadin gwiwa da kasashen da wannan ziri da kuma hanya suka tsara su tare da yayata hadin gwiwa tsakanin yankuna, ta hanyar gudanar da muhimman ayyuka kamar layin dogo, hanyoyin mota, harkokin jiragen sama. Sauran sun hada da hasken wutar lantarki da harkokin sadarwa.
Kasar Sin ta bullo da wannan shiri ne a shekarar 2013, da nufin bunkasa harkokin kasuwanci da samar da muhimman kayayyakin more rayuwa wadanda za su hade yankunan Asiya da Turai da Afirka da suka tsara ta tsoffin hanyoyin da ake cinikin siliki. (Ibrahim)