Ma Kai ya yi wannan kira ne yayin taron majalisar gudanarwar kasar, inda ya ce, har yanzu kasar na fuskantar matsala game da ayyukan yi, al'amarin da ya ce akwai bukatar hukumomi su kara zage damtse wajen shiryawa da tsara yadda za a magance matsalar.
Ya ce akwai bukatar bunkasa ayyukan masana'antu da kamfanoni ta yadda za a samar da karin guraben aikin yi, da karfafawa mutane fara sana'a a kansu, tare da ba da horo kan sana'o'in hannu.
A bara dai, kasar Sin ta samar da guraben aikin yi miliyan 13.1 ga mazauna birane. Duk da haka, zuwa karshen shekarar, adadin marasa aikin yi dake da rajista a biranen kasar ya kai kashi 4 cikin dari. (Fa'iza Mustapha)