in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijeria: jihar Rivers mai arzikin man fetur ta yi maraba da masu zuba jari
2017-03-11 12:35:28 cri
Jihar Rivers mai arzikin mai a Nijeriya, ta gayyaci masu zuba jari, su yi amfani da damar ci gaban da ake samu a jihar wajen zuba jari a dukkan bangarorin tattalin arziki, domin samar da guraben aikin yi.

Da yake ganawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a jihar Lagos, Kwamishinan yada labarai na jihar Rivers, Austin Tam-George ya ce wannan ne karon farko da masu zuba jari za su samu wani tsarin haraji mai sauki da kuma damar isa yankunan kasa na jihar cikin sauki.

Kwamishinan ya ce an samar da wasu kyawawan tsare-tsare ciki har da sahalewa masu zuba jarin cikin sa'o'i 48, yana mai cewa sun kuma ba da tabbacin tsaron lafiyar masu zuba jari.

Ya ce masu zuba jarin za su samu damar neman dimbin albarkatun man fetur da iskar gas da ke akwai a jihar, yana mai cewa zai zama wani aiki na hadin gwiwa da zai samar da guraben aikin yi tare da bunkasa bangaren masana'antu a Nijeriya.

Tam-George ya ce Gwamnatin jihar na bada muhimmanci sosai ga tsaron rayuka da dukiya da samar da ababen more rayuwa da ilimi, kuma kiwon lafiya.

Har ila yau, Kwamishinan ya ce Gwamnatin ta kuduri aniyar farfado da tattalin arzikin jihar, ta yadda zai dore tare da fadada bada damarmaki ga kowa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China