in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Muhimman labarai daga wasu jaridun Najeriya
2017-02-24 19:46:21 cri

A jiya ne babban bankin Najeriya(CBN) ya sake dawo da kudaden da bankuna a sassa daban-daban na kasar za su rika caja kan kudade da ake ajiyewa a asusun ajiyarsu, sai dai matakin zai fara ne a mabanbantan lokuta a bankunan sassan kasar.(Vangaurd)

A jiya Alhamis ne wasu bata gari suka fake da zanga-zangar lumanan da wasu dalibai suka shirya a Abuja, inda suka mamaye katafaren ofishin kamfanin sadarwa mallakar kasar Afirka ta kudu, MTN, kana suka barnata wasu kayayyaki tare da yin awon gaba da wayoyin salula,da kwafutocin tafi da gidanka gami da wasu kayayyaki. Wannan ya biyo bayan rahotannin hare-haren nuna kyamar baki da ya rutsa da wasu 'yan Najeriya a kasar ta kudu a 'yan kwanakin nan.(Punch)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China