in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya tana fatan janyo jarin dala biliyan 10 a bangaren man kasar
2017-03-01 10:05:18 cri
Karamin ministan albarkatun mai na tarayyar Najeriya Ibe Kachikwu ya bayyana cewa, a cikin shekaru biyar masu zuwa kasarsa tana fatan janyo jarin da ya kai tsabar kudi dala biliyan 10 a bangaren mai da iskar gas na kasar.

Ministan wanda ya bayyana hakan yayin da ya ke jawabi a yayin wani taro da baje koli na kasa da kasa da aka bude a Abuja, fadar mulkin kasar, ya ce duk da tarin matsalolin da kasar ta ke fuskanta ciki har da ayyukan masu tayar da kayar baya a yankin Niger Delta, gwamnatin Najeriyar tana kokarin ganin ta kara janyo masu sha'awar zuba jari a cikin kasar.

Ministan ya ce, idan har kasar ta samu nasarar cika wannan buri, hakan zai taimakawa kasar wadda ke kan gaba wajen samar da mai a nahiyar Afirka magance wasu daga gibin da bangaren mai da iskar na kasar ya ke fuskanta.

Yanzu haka bangaren da ke tace albarkatun man kasar ya bullo da karin matakai tare da kara yawan jari domin farfado da bangaren, a wani mataki na ganin kasar ta cimma bukatunta na mai na cikin gida tare da zama kasar dake fitar da tacaccen mai zuwa ketare.

Ministan ya ce tun a watan Yulin da ya gabata ne aka fara samun daidaito a masana'antun tace man kasar, amma dai har yanzu ana ci gaba da aikin magance kalubalen da sashen ya ke fuskanta.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China