Gwamnatin Nijeriya na shirin zuba wani bangare na kudaden da wasu tsoffin jami'anta suka wawure cikin shirye-shiryenta na tallafawa jama'a.
Wani babban jami'in gwamnatin kasar ya shaidwa jaridar Punch cewa, za a yi amafani da dala miliyan tara da aka kwato daga tsohon shugabn kamfanin mai na kasar NNPC, da dala miliyan dari da hamsin da uku na tsohuwar Ministan albarkatun mai a shirye-shiryen gwamnati na taimakawa talakawa.( Jaridar Punch).
Fadar Shugaban kasar Nijeriya ta ki cewa komai game da ainihin ranar da shugaba Muhammadu Buhari zai koma gida, daga hutun da ya tafi domin duba lafiyarsa a London. Zuwa yau Lahadi, shugaban ya shafe tsawon kwanaki 32 cif a Birtaniya.
Mataimakin shugaban kasar kan harkokin yada labarai Femi Adeshina, ya ce shugaban ba sulalewa zai yi ya shigar kasar ba idan ya dawo, yana mai cewa a duk fadin kasar ne aka zabe sa, don haka, dawowarsa ba za ta zama abun sirri ba, yana mai cewa idan ya dawo, al'ummar kasar baki daya za su sani. ( Daily Trust) ( Fa'iza Mustapha)