Kakakin Rundunar 'yan sandan jihar Lagos dake kudu maso yammacin kasar Joseph Alabi, ya ce 'yan Nijeriyar da a aka mai da gida, sun isa Lagos din ne da yammacin ranar Talata, kasa da makonni biyu ke nan, bayan hukumomin Italiyar sun mayar da wasu 'yan kasar 33 bisa zarginsu da aikata makamancin wancan laifi.
Jami'an hukumar kula da shige da fice na kasar da takwarorinsu na hukumar yaki da safarar bil'adama da na rundunar 'yan sanda ne suka karbi mutanen da suka kasasnce maza duka.
Jami'an hukumar shige da fice ne suka dauki bayanansu, kana suka shirya yadda za a mai da su garuruwansu.(Fa'iza Mustapha)