in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sudan ta kudu ya kori gwamnan babban bankin kasar
2017-01-16 10:21:34 cri
Da yammacin ranar Asabar da ta gabata ne, shugaban kasar Sudan ta kudu Salva Kiir, ya sallami gwamnan babban bankin kasar na Sudan ta kudu BSS, a daidai lokacin da kasar ke tsaka da fuskantar tsadar farashin kayayyaki da rikicin tattalin arziki.

Kiir, ya maye gurbin gwamnan babban bankin kasar Kornelio Koryom Mayik, inda nan take ya nada tsohon daraktan musayar kudaden waje Othom Rago Ajak, kamar yadda gidan radiyon kasar ya tabbatar da hakan.

Sai dai shugaban kasar bai bayyana dalilan da suka sa ya kori Mista Mayik ba, sai dai ana rade radin cewar, korar jami'in ba zai rasa nasaba da yadda gwamnatin ta gaza hakuri ba, game da tsadar farashin kayayyaki da kuma karyewar darajar kudin kasar dake cigaba da faduwa saboda rashin daukar matakain kayyade farashi a kasuwar musayar kudaden kasashen waje tun daga watan Disambar 2015. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China