Sanarwar ta ce, rundunar ta lura da labarun da kafofin watsa labaru ke bayarwa, inda aka cewa, gwamnatin Sudan ta kudu na adawa da batun girke rundunar sojin.
Sanarwar ta ruwaito cewa, har zuwa yanzu, kasar na fuskantar tashe-tashen hankula, inda fararen hula da dama ke cikin matsalar rashin tsaro.
A ranar 11 ga wata ne, kakakin gwamnatin kasar Sudan ta Kudu Michael Makuei Lueth ya bayyanawa manema labaru cewa, an samu kyautatuwar tsaro a Juba, babban birnin kasar da yankunan dake kewayensa, a don haka, gwamnatin kasar ba za ta karbi shirin girke rundunar sojin ba da kariya a kasar ba. (Bilkisu)