in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana bikin cikar Ghana shekaru 60 da samun 'yancin kai
2017-03-07 09:44:30 cri

An fara shagulgulan cikar kasar Ghana shekaru 60 da samun 'yancin kai a birnin Accra, fadar mulkin kasar. An dai gudanar da fareti na musamman a filin taro na "Independence Square", wanda ya samu halartar manyan baki daga sassan duniya daban daban, baya ga 'yan kasar da suka yi fitar 'dango domin halartar bikin.

Rahotanni sun bayyana cewa, 'yan makarantu, da jami'an tsaro na cikin wadanda suka shiga faretin da ya gudana. Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe na cikin shugabannin kasashe da suka ganewa idanun su yadda wannan biki ya wakana.

Da yake jawabi gaban dubban mahalarta bikin, shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo-Addo, ya ce bayan shekaru 60 Ghana na fakewa da wasu uzurori, yanzu lokaci ya yi da al'ummar kasar za su zage mantse wajen daga matsayin kasar su a idanun duniya.

Shugaba Akufo-Addo ya ce, babban kalubalen dake gaban 'yan kasar shi ne, na sake bunkasa tattalin arziki da inganta zamantakewa da rayuwar talakawan kasar.

Ghana ce dai kasar farko a yankin kudu da hamadar Saharar Afirka, da ta samu 'yancin kan ta daga Turawan mulkin mallaka a yankin.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China