in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ghana na shirin zama rumbun abinci a nahiyar Afrika
2017-03-02 09:52:58 cri

Ministan aikin gona na kasar Ghana Afriyie Osei Akoto ya bayyana cewa, sabon tsarin aikin gona da kasar za ta kaddamar wata mai zuwa, na shirin mai da rumbun abinci a nahiyar Afrika.

Da yake jawabi yayin wani taro kan shirin ciyar da bangaren noma, da inganta samun riba, wato ADVANCE a takaice, da ya gudana jiya, ministan ya ce, sabon tsarin zai mai da hankali ne ga kananan manoma dubu dari biyu, da kuma kayayyakin abinci biyar da suka hada da waken soya, da dawa, da masara, da shinkafa, da kuma kayan lambu.

Ya ce, ana sa ran shirin zai lakume kudin cedi na Ghana miliyan dari biyar da sittin kwatankwacin dalar Amurka miliyan dari da ashirin. Sannan, ana sa ran zai samar da cedi biliyan 1.3 na kudin shiga ga manoman da suka shiga shiri, baya ga ayyuka a kalla dubu dari bakwai da hamsin da zai samar.

ADVANCE, shiri ne da aka samar da shi karkashin shirin Feed the Future da hadin gwiwar hukumomin raya kasashe ke aiwatarwa a Ghana bisa jagoranccin hukumar raya kasashe ta Amurka USAID.

A mataki na biyu da shirin ke ciki yanzu, ya mai da hankali ne kan manoma dubu dari da goma sha uku a wasu fannoni dake da nufin bunkasa wasu yankuna.

Mataimakin shugaban shirin na USAID Steven Hendrix ya ce, Ghana tana da damar da za ta iya zama rumbun abinci a nahiyar Afrika. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China