in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An shirya liyafar murnar bikin ranar mata ta duniya
2017-03-07 20:33:55 cri
Da yammacin yau Talata ne a nan Beijing aka shirya wata liyafa domin murnar bikin ranar mata ta duniya.

A yayin liyafar, Shen Yueyue, shugabar hukumar kula da harkokin mata ta kasar Sin ta taya wa mata daga sassa daban daban na duniya murnar bikin ranar mata ta duniya, inda ta bayyana cewa, kasar Sin na son hada kai da mata daga sassa daban-daban na duniya ta yadda za a samar da kyakkyawar makomar dan Adam.

Mata fiye da dubu 1 ne daga bangarorin daban-daban na kasar Sin da ma na kasashen waje wadanda suke aiki ko yin zama a nan kasar Sin sun halarci liyafar. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China