Game da wannan, 'dan jaridar rediyon kasar Kenya Eric Biegon ya bayyana wa 'yan jaridun gidan rediyon kasar Sin CRI cewa, fasahohin da kasar Sin ta samu wajen kawar da talauci, sun cancanci kasashen Afirka su yi koyi da su.
Eric Biegon ya kara da cewa, a cikin rahoton an gabatar da cewa, kamata ya yi a gudanar da ayyukan kawar da talauci bisa halin musamman, kuma a bana kasar Sin za ta kara rage matalauta sama da miliyan 10 a kauyuka. Wannan ya nuna cewa, gwamnatin kasar Sin ta mayar da hankali sosai kan shawarwarin da wakilai bisa matsayi daban daban na kasar suke gabatarwa game da yadda ake kokarin rage matalauta a birane da kauyuka, da kara samar da guraban aikin yi, da kuma inganta kyautatuwar zaman rayuwar jama'a. (Bilkisu)