Ministar shara'a ta kasar Burundin Aimee Laurentine Kanyana, ita ce ta kaddamar da shirin a gidan yari na Mpimba dake Bujumbura babban birnin kasar.
Wannan afuwar da shugaban kasar Burundin Pierre Nkurunziza ya yi, ya sanar da yinta ne a cikin jawabinsa na sabuwar shekara.
Ministar ta ce daga cikin wadanda aka yiwa afuwar akwai mutane 58 daga jam'iyyar hamayya ta (MSD). Haka zalika, cikin wadanda afuwar ta shafa akwai 'yan ta da kayar baya da suka shiga zanga zangar nuna adawa da takarar shugaba Nkurunziza a watan Afrilun shekarar 2015.
Madam Aimee tace wadanda afuwar shugaban kasar ta shafa su ne mazauna gidajen yarin da laifukansu ba su kai daurin shekaru biyar ba, da kuma wadan da suka shafe kashi 3 bisa kashi 4 daga cikin adadin shekarun da aka debar musu, kana mutanen dake nuna halin da'a yayin da suke cikin kurkuku.(Ahmad Fagam)