Kwamishinan kula da harkokin zaman lafiya da tsaro na kungiyar AU Smail Chergui shi ne ya bayyana hakan, yayin wani taron manema labarai a birnin Bujunbura, fadar mulkin kasar Burundi.
Jami'in na AU ya ce wannan mataki zai kara karfafa gwiwar dakarun kungiyar AU da ke aikin kiyaye zaman lafiya a sassa daban-daban na duniya.
A jawabinsa mataimakin shugaban kasar Burundi na farko Gaston Sindimwo ya bayyana farin cikinsa dangane da matakin AUn na ganin an biya sojojin kasar hakkokinsu.
A yayin da yake kasar ta Burundi, jami'in kungiyar ta AU ya kuma gana da masu sanya ido na kungiyar tarayyar Afirka da kwararru a fannin aikin soja da ke kasar.
Bugu da kari Chergui ya ziyarci makabartar Mpanda mai nisan kilomita 12 arewa da babban birnin kasar, inda ya nuna girmamawa ga dakarun wanzar da zaman lafiya na AMISON da suka kwanta dama yayin da suke fagen daga.
Sai dai a sakonsa na murnar sabuwar shekara da ya gabatarwa 'yan kasa shugaba Pierre Nkurunziza na Burundi, ya ce gwamnatinsa za ta kai karar kungiyar AU saboda rashin biyan hakkokin sojojin kasar da suka yi aiki karkashin laimar AMISON. Kasar ta Burundi dai ta tura sojoji kimanin dubu 5 zuwa kasar Somaliya, domin maido da zaman lafiya sakamakon hare-hare da mayakan al-Shabaab ke kaddamarwa a sassa daban-daban na kasar
Ziyarar Chergui a kasar ta Burundu dai tana zuwa ne a daidai lokacin da kasar take barazanar janye dakarunta daga kasar Somaliya.(Ibrahim Yaya)