in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan majalissar Burundi sun yi watsi da zargin take hakkin bil Adama da ake yiwa kasar
2017-01-23 10:39:05 cri
'Yan majalissar dokokin kasar Burundi, sun yi watsi da zargin da kungiyar tarayyar turai ta yiwa mahukuntan kasar, na keta hakkokin bil Adama, suna masu cewa, ko alama kungiyar ta EU ba ta san hakikanin halin da ake ciki a kasar ba.

Cikin wata sanarwar da mai magana da yawun majalissar Alexis Badian Ndayihimbaze ya fitar a ranar Asabar din makon jiya, ya ce abu mafi dacewa shi ne EU ta tura wakilai, domin ganin halin ci gaba da aka samu a kasar Burundi a fannin tsaro, da siyasa, da ma zamantakewar al'umma.

Game da batun dokar ayyukan kungiyoyi masu zaman kan su da majalissar ta sanyawa hannu a watan Disambar bara kuwa, Mr. Ndayihimbaze ya ce burin majalissar shi ne, irin wadannan kungiyoyi su rika aiki bisa doka, tare da kayyade hurumin gwamnati cikin ayyukan su, da ma batun irin tsarin kashe kudaden su.

Ya ce ga misali, dokar ta tanaji cewa kungiyoyi masu zaman kan su na kasashen ketare, za su biya gwamnati dala 500, a matsayin kudin tsara musu yadda za su tafiyar da ayyukan su cikin nasara. Kana dole kungiyoyin su bude asusun ajiya na kudaden waje da babban bankin kasar, amma su rika biyan ma'aikatan su albashi da kudin kasar na Burundi franc domin kare darajar kudin.

A hannu guda kuma, su rika kare martabar halayya da al'adun al'ummar Burundi, da daidaiton jinsi, da kwarewar ma'aikata, kamar yadda kundin mulkin kasar ya tanada.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China