Da yake karanta jawabin gwamnatin Burundi, mataimakin ministan harkokin cikin gida Therence Ntahiraja ya ce, suna kira ga shugabannin kungiyar tarayyar Afrika (AU) dake taro a Habasha a ranar 31 ga watan nan, da MDD da su yi watsi da rahoton da majalisar dokokin Turai ta fitar wanda babu komai cikinsa sai karairayi da ruruta wutar rikici da kuma jita jita.
Wannan zanga zanaga an gudanar da ita a duk fadin kasar, kuma jami'an gwamnatin kasar sun bi sahun jama'a don gudanar da zanga zangar.
A ranar 19 ga watan Janiru ne, majalisar dokokin Turai ta gabatar kuduri inda ta nuna wasu batutuwa da suka shafi cin zarafin bil adama a kasar Burundin.
To sai dai kuma, gwamnatin kasar Burundi, da majalisar dokokin kasar sun yi watsi da wannan rahoto, inda suka bayyana shi da cewa garyace tsagwaronta. (Ahmad)