Da yake gabatar da rahoton ayyukan gwamnatin kasar ga taron wakilan jama'ar kasar, Li Keqiang, ya ce samar da kwanciyar hankali na da muhimmanci gaya, inda ya ce dole ne a kiyayi kai wa matakin gargadi na rashin kudi, tare da tabbatar da kare muhalli da zamantakewar al'umma.
Rahoton ya ce a kokarinta na cimma wadannan muradu, kasar Sin za ta matse kaimi wajen aiwatar da sauye-sauye da za su kai ta ga samun nasarori a muhimman bangarori. (Fa'iza Mustapha)