in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar wakilan jama'a ta kasar Sin ta bukaci a zurfafa yaki da munanan laifuka
2017-01-12 11:15:58 cri

Zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin NPC da hukumominsa na dukkan matakai, za su zurfafa aniyar tsabtace sha'anin gwamnati da kuma yaki da laifuka, kamar yadda jami'an majalisar suka tabbatar da hakan a jiya Laraba.

Sanarwar ta bayyana muhimman shawarwari da aka cimma a lokacin taron, wanda babban kwamitin wakilan jama'a ya gudanar a ranar Litinin. Mahalarta taron sun nazarci muhimman bayanan da aka amince da su, a lokacin zama na 7 na taron hukumar lataftarwa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar CPC karo na 18.

Kwamitin na NPC ya amince da wadannan kudurori karkashin jagorancin babban daraktan jam'iyyar CPC na kasar Sin shugaba Xi Jinping, domin tabbatar da ganin an aiwatar da tsare-tsare da manufofin da aka zartar karkashin kwamitin tsakiya na CPC, wanda majalisar wakilan jama'a da zaunannen kwamitin wakilan za su aiwatar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China