in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan majalisa dokokin kasar Sin sun kamala taron su na wannan karon
2016-02-27 13:51:33 cri
Zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin wato NPC ta kamala taron ta da ta kan yi a watanni biyu biyu a ranar jumma'an nan wanda tayi shirye shiryen babban taron majalissar dokokin kasar dake tafe na shekara shekara.

Zhang Dejiang shugaban kwamitin ne ya jagoranci bikin rufe taron na kwanaki uku.

Yawancin 'yan majalissar dokokin sun amince da daftari akan aikin kwamitin na NPC, wanda za'a gabatar a wajen taron shekara shekara bayan da aka yi wassu 'yan kwaskwarima akan shi.

Yawancin 'yan majalissar sun amince da aikin kwamitin a cikin shekarar da ta gabata, inji Mr Zhang a wajen rufe taron.

Haka kuma a wajen taron. Majalissar ta amince da dokar farko na kasar akan amfani da albarkatun cikin ruwa wanda keda nufin kyautata muhallin teku da tabbatar amfani da albarkatun cikin inganci yadda ya kamata.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China