in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gudanar da taron zaunannen kwamitin majalisar NPC karo na 23 kan batun magudi
2016-09-13 19:30:37 cri

Shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin na NPC na 12 Mr. Zhang Dejiang, ya jagoranci taro na zama na 23 a ranar Talatar nan. Zaman dai na da nufin nazartar batun magudi da ake zargin an tafka, a yayin zaben da ya gudana a lardin Liaoning dake arewa maso gabashin kasar Sin.

Wata sanarwa da aka fita ta bayyana cewa, kwamitin majalisar ya yi amfani da taron na wannan karo, wajen aiwatar da shawarar da JKS ta yanke game da batun zaben lardin na Liaoning, domin sauke nauyin aiki dake wuyan zaunannen kwamitin.

Zaunannen kwamitin majalisar NPC karkashin JKS na zaman sa ne sau biyu a ko wane wata, sai dai kuma yana iya shirya wani zama na daban idan har akwai bukatar hakan. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China