in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar Sin
2017-03-05 09:09:29 cri

Da misalin karfe 9 na safiyar yau Lahadi da safe agogon Beijing ne, Mr. Zhang Dejiang, shugaban kwamitin dindindin na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, wato majalisar kafa dokokin kasar ya shelanta kaddamar da taron shekara-shekara na majalisar a nan Beijing.

Shugaba Xi Jinping da sauran kusoshin kasar na daga cikin wadanda suka halarci bikin kaddamar da taron.

A yayin bikin kaddamarwar, firaministan gwamnatin kasar Sin Li Keqiang ya gabatar da wani rahoto game da aikin da gwamnatin kasar Sin ta yi a shekarar ta 2016 da kuma za ta yi a bana.

A cikin kwanaki 10 masu zuwa, wakilan jama'a kusan dubu 3 za su sauke nauyin dake wuyansu na tattauna wannan rahoto. daga bisani kuma su amince da shi. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China