Saleh Bozreba, jagoran kungiyar ta Red Crescent mai yunkurin wanzar da zaman lafiya a Misrata, yace, gawarwaki 65 daga cikin adadin da aka gano, mayakan kungiyar IS ne, wadan da aka kashe a sanadiyyar hare hare ta sama da jiragen yakin Amurka suka kaddamar a ranar 19 ga watan Janairu a kudancin Sirte.
Bozreba yace har yanzu jami'an sa kai na kungiyar Red Crescent suna cigaba da aikin gano ragowar gawarwakin a Sirte, sai dai ya bukaci kungiyoyin kasar Libya da na kasa da kasa da su agazawa tawagar.
Sirte, nada tazarar kilomita 450 dake gabashin Tripoli babban birnin kasar, kuma ya kasance a hannun mayakan IS sama da shekara guda kafin daga bisani dakarun dake biyayya ga gwamnatin Libya mai samun goyon bayan MDD su kwace ikon birnin bayan shafe watanni 7 suna gwabza yaki.
Rikicin ya haddasa mutuwar da kuma raunatar daruruwan jami'an gwamnati.(Ahmad Fagam)