in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin musamman na MDD ya kai ziyara Libya
2017-01-09 11:15:08 cri
Jiya Lahadi 8 ga watan nan ne, wakili na musamman na sakatare-janar na Majalisar Dinkin Duniya, kana shugaban tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD a Libya wato UNSMIL, Mista Martin Kobler, ya isa Tripoli, fadar mulkin kasar, inda ya yi shawarwari tare da firaministan gwamnatin hadaka ta kasar Libya Fayes al-Sarraj.

Bangarorin biyu sun tattauna game da wasu muhimman batutuwa, ciki har da harkokin siyasar kasar, gami da kyautata yanayin zaman rayuwar al'umma.

Dadin dadawa, a wajen taron manema labarai da aka yi, Martin Kobler ya jaddada cewa, kamata ya yi a ba da fifiko kan tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali ga jama'ar kasar ta Libya.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China