in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Libya ta ware dalar Amurka biliyan 3.43 don magance matsalar tattalin arziki
2017-01-24 13:42:02 cri
Kakakin gwamnatin kasar Libya ya bayyana a jiya Litinin cewa, babban bankin Kasar ya ware Dinar Biliyan 4.8, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 3.43 wajen magance halin matsi da tattalin arzikin kasar ke ciki.

Ashraf Al-Thulthi, kakakin gwamnatin hadin kan al'ummar kasar da MDD ke marawa baya, ya gudanar da wani taron manema labarai, inda ya ce gwamnati na kokarin magance matsalar karancin lantarki da ake fuskanta a kasar, yana mai cewa, an dawo da samar da gas ga tashoshin lantarkin.

Baya ga matsalar ayyukan 'yan tawaye, kasar Libya, na fuskantar matsaloli da suka hada da matsin tattalin arziki da siyasa, inda take da gwamnatoci daban-daban dake adawa da juna har guda uku.

Al-Thulthi ya ce har yanzu, kamfanonin kasashen waje ba su dawo da yin aikin da aka dakatar na tashoshin lantarki ba, al'amarin da ya ce na kara ta'azzara matsalar karancin lantarki.

Kakakin ya kuma yi kira ga al'ummar kasar, su rage yadda suke amfani da lantarkin, wanda ya ce zai taimaka wajen warware matsalar.

Ya kuma yi tir da harin bam da aka kai tsakiyar birnin Tripoli cikin mota a ranar Asabar, al'amarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu. ( Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China