Da yake mai da martani game da rahoton a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai Rabe Abubakar, ya ce rahoton na Amnesty shirme ne kawai. Ya ce, yana fatan al'umma za su yi fatali da shi, ganin cewa, a baya ma kungiyar ta Amnesty, ta sha fidda irin wannan rahoto, inda take zargin sojoji da sauran jami'an tsaron kasar da aikata laifuka, ba tare da wata hujja mai karfi ba.
Kaza lika Rabe ya zargi Amnesty International da kitsa bayanai marasa kan gado domin cimma wata manufa ta daban, da kuma yunkurin haifar da rashin hadin kai da tsana tsakanin 'yan Najeriya.
A hannun guda kuma gwamnatin Najeriyar ta ce ba ta ji dadin yadda kungiyar Amnesty wadda ya kamata a ce ta tsame kanta daga harkokin siyasa, sannan ta rika ba da rahoto ba tare da nuna son kai ba, amma ita ce ta ke irin wannan katubara.(Ibrahim)