Ministan wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwar da aka rabawa manema labarai a birnin Legas, ya ce an dauki wannan mataki ne da nufin kawar da duk wani shige da masu sha'awar yin harkokin kasuwanci da yawon shakatawa a cikin kasar ke fuskanta, ta yadda hakan zai bunkasa tattalin arzikin kasar.
Minista Lai ya kara da cewa, wannan wani bangare ne cikin jerin matakan da gwamnati ta tsara da nufin saukaka harkokin kasuwanci da bunkasa yawon bude ido, karkashin shirin mahukuntan kasar na fadada sassan tattalin arzikinta.
Yanzu haka dai hukumar shige da ficen kasar (NIS) ta fara nazartar ka'idojin samun takardar iznin shiga kasar, a wani mataki na fara janyo masu sha'awar gudanar da huldar arziki a cikin kasar. (Ibrahim Yaya)