in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Buhari ya yi kira ga 'yan Najeriya da su kwantar da hankulansu
2017-02-22 09:16:51 cri
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya bukaci al'ummar kasarsa da su kwantar da hankulansu, game da batun tsawaitar zamansa a Birtaniya, yana mai cewa babu dalilin da zai sanya a shiga damuwa.

Wata sanarwar da kakakin fadarsa Femi Adesina ya fitar, ta bayyana cewa, ba a sanya wani lokaci na komawar shugaban na Najeriya gida ba. Sai dai ta bayyana cewa Buhari na da bukatar kara hutawa, bisa shawarar likitansa.

Tsawaitar wa'adin da shugaban na Najeriya ya kwashe yana hutu na ci gaba da ta da kura, inda da yawa daga masu adawa da gwamnatinsa ke cewa, ya kamata a fayyace gaskiyar lamari game da yanayin lafiyar shugaban.

Kafin barinsa Najeriya, shugaba Buhari ya mika takarda ga majalissar dattijan kasar, yana mai bukatar baiwa mataimakinsa Yemi Osinbajo, damar ci gaba da jan akalar kasar, har zuwa lokacin da zai koma gida, kamar dai yadda hakan ke kunshe cikin kundin mulkin kasar. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China