in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An cafke wasu kusoshin kungiyar Boko Haram
2017-02-22 10:19:01 cri
Gwamnan jihar Kogi dake tsakiyar Najeriya Yahaya Bello, ya ce jami'an tsaron kasar sun cafke wasu kusoshin kungiyar Boko Haram su hudu a jihar ta Kogi bayan samun wasu bayanan sirri.

Da yake tsokaci game da hakan a birnin Abuja fadar mulkin kasar, gwamna Bello, ya ce an cafke mayakan Boko Haram din ne a shekaranjiya Litinin, ana kuma zaton 'ya'yan kungiyar na yunkurin sake taruwa ne a jihar, bayan da dakarun sojin kasar suka fatattake su daga yankin arewa maso gabashin kasar.

Sai dai fa gwamnan na jihar ta Kogi ya ce masu tada kayar bayan sun makara, domin kuwa gwamnatinsa, da hadin kan sassan jami'an tsaron kasar, za su yi duk mai yiwuwa, wajen tabbatar da cewa hakar su bata cimma ruwa ba.

Daukar wannan mataki ko shakka babu, zai tabbatar da nasarar da dakarun sojin Najeriya suka samu a yakin da suke yi da 'yan Boko Haram a arewa maso gabashin kasar, kamar dai yadda gwamnan ya bayyana. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China