in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu mahara sun kaiwa sojojin Nijer hari
2017-02-28 09:32:43 cri
Hukumomin tsaro a kasar Nijer sun bayyana cewa, jiya da safe wasu dakarun da ba a san asalinsu ba sun kaiwa sojojin gwamnatin kasar Nijer hari a yankin Agadez dake arewacin kasar, harin da ya haddasa rasuwar sojoji a kalla guda 16.

Bayanai na nuna cewa, sojojin da dakarun suka kashe, sojojin kota-kwana ne wadanda aka girke a wani sansanin ba da horon soja dake kusa da babban birnin kasar, Niamey. Kuma suna kan hanyarsu ce ta koma wa sansaninsu a lokacin da aka kai musu harin.

Ya zuwa tsakar ranar jiya dai, gwamantin Nijer din ba ta yi wani karin bayani game da harin da ya auku ba, kuma babu wata kungiya da ta sanar da daukar alhakin kai harin. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China