in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
A Nijeriya: an ji fashewar wasu abubuwa a tsohuwar maboyar kungiyar Boko Haram
2017-01-14 12:53:25 cri
Wani jami'in yankin, ya shaidawa Kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, da safiyar jiya Juma'a, wasu abubuwa sun fashe har sau uku a garin Madagalin jihar Adamawa dake yankin arewa maso gabashin Nijeriya,wanda a baya ya kasance maboyar 'ya'yan kungiyar Boko Haram.Sai dai kawo yanzu, ba a san adadin wadanda al'amarin ya rutsa da su ba.

Shugaban karamar hukumar Madagali Yusuf Mohammad, ya ce an ji karar fashewar ne a wani shingen binciken sojoji dake mashigar garin, wanda ke makwaftaka da dajin Sambisa, wato tsohon sansanin kungiyar Boko Haram dake jihar Borno.

Dan majalisar dokokin kasar mai wakiltar Madagali Adamu Kamale, ya yi kira ga gwamnati, ta tura krin sojoji yankin da a cewarsa 'yan tada kayar baya da suka tsere ke samun mafaka. ( Fa'iza Mustapha )

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China