in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun Najeriya sun kwace dajin Sambisa daga hannun Boko Haram
2016-12-25 13:25:34 cri

A jiya Asabar shugaban Najeriya Muhammadu ya sanar da cewa, sojojin kasar dake yaki da mayakan Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar, sun yi nasarar fatattakar mayakan Boko Haram daga babbar maboyarsu dake dajin Sambisa.

A wata sanarwa da aka baiwa kamfanin dillancin labarai na Xinhua, shugaban na Najeriyaa ya taya sojojin kasar murna, bisa nasarar da suka samu na kwace ikon dajin Sambisa wanda ya kasance babbar maboyar mayakan na Boko Haram.

Buhari ya ce, ya yi matukar nuna farin cikinsa, bisa wannan nasarar da dakarun kasar suka samu.

Ya ce, ya yi matukar murna, kuma wannan abin alfahari ne irin bajintar da dakarun kasar suka nuna, labari ne mai dadin ji cewa an kwace dajin Sambisa wanda aka jima ana sa tsammani hakan, kuma shi ne maboya ta karshe na mayakan Boko Haram.

Buhari ya kara da cewa, shugaban rundunar sojin kasar ya sanar da shi da misalin karfe 1:35 na yammacin ranar Alhamis wato 22 ga watan nan na Disamba cewa, mayakan 'yan ta'adda suna tserewa, kuma a yanzu ba su da sauran wajen buya.

Shugaban ya kuma bukaci dakarun kasar da su cigaba da gudanar da aikinsu na fatattakar 'yan ta'adda da kuma gurfanar da su a gaban shari'a.

Shugaba Buhari ya bukaci 'yan Najeriya da su taimakwa sojojin kasar da sauran jami'an tsaro wajen sanar da su muhimman bayanai game da 'yan ta'adda dake neman mafaka a cikin jama'a.

Kana ya bukaci dakarun kasar da su kara azama domin kwato ragowar 'yan matan Chibok da mayakan ke tsare da su.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China