Wata sanarwa da rundunar sojojin kasar ta rabawa manema labarai a Yau Talata ta bayyana cewa, matakan soja da dakarun kasar suke ci gaba da aiwatar a sansanin mayakan na camp Zero, wata alama ce dake nuna cewa, sojojin kasar sun yi nasarar kama hedkwatar kungiyar.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ayyana cewa, dakarun kasar sun yi nasarar murkushe kungiyar, lamarin da ya tilasta musu arcewa daga dajin, baya ga wasu kuma da ka kama.
A nasa bangare babban hafsan sojojin kasa na Najeriya, Laftana janar Tukur Buratai, ya ce daga shekarar 2017, za a rika amfani da dajin na Sambisa a matsayin wurin horas da sojojin kasar.
Buratai ya bayyana hakan ne a garin Damasak,yayin bikin kirsimati da ya yi da dakarun bataliya 145, bayan da gwamnan jihar Borno Kashim Shettima ya sake bude hanyar da ta taso daga Maiduguri zuwa Gubio zuwa garin na Damasak da aka rufe shekaru uku da suka gabata.
Yanzu haka dai dakarun kasar suna gudanar da sintiri a dajin, tun bayan da kwace tungar kungiyar ta karshe. Don haka ya bukaci sojojin da su ci gaba da farautar makayan Boko Haram din da suka gudu don ganin an kama su.(Ibrahim)