in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da littafi mai kunshe da zababbun takardun taron koli na G20 a Hangzhou
2017-02-27 11:02:36 cri

A kwanan baya ne, aka kaddamar da wani littafi mai kunshe da zababbun takardun da aka gabatar a taron kolin shugabannin kasashen kungiyar G20 da ya gudana a birnin Hangzhou na kasar Sin.

Shi dai wannan litattafi, ana sayar da na Sinancinsa a nan kasar Sin yayin da ake sayar da wanda aka fassara cikin harshen Turanci a kasashen waje.

An samu nasarar gudanar da taron kolin G20 karo na 11 a watan Satumban bara ne a birnin Hangzhou, inda aka samu sakamako da dama, wadanda ba a taba ganin irinsu a baya ba. Taron ya kuma tsara ajandar bunkasa tattalin arzikin kasa da kasa, ya kuma sanya halin musamman na kasar Sin kan yadda za a farfado da tattalin arzikin duniya. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China