in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron masu bibiyar taron kolin G20 na shekarar 2016 karo na 5
2016-10-27 19:58:53 cri
An bude taron masu bibiyar taron kolin kungiyar G20 na shekarar 2016 karo na 5 a birnin Wuhan dake kasar Sin a yau alhamis, inda jagoran jami'an bibiyar harkokin kungiyar ta G20 na kasar Sin, kuma mataimakin ministan harkokin wajen kasar Li Baodong ya shugabanci taron.

Da yake jawabi yayin bude taron, Li Baodong ya bayyana cewa, an rufe taron kolin G20 na birnin Hanzhou cikin nasara, tare da bayar da sanarwar shugabancin taron, inda aka tabbatar da makomar hadin gwiwar membobin G20, da burin da aka sa gaba, da matakan da za a dauka.

Muhimmin aikin taron masu bibiyar a wannan karo shi ne sa kaimi ga aiwatar da ayyukan da aka amincewa, a gun taron kolin na G20 na Hangzhou, da mika aiki ga kasar Jamus, wadda ita ce za ta karbi bakuncin taron a karo mai zuwa. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China