Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta sanar a Talatar nan cewa, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, zai kai ziyara kasar Jamus tsakanin ranekun 15 zuwa 18 ga watan nan, domin halartar kwarya-kwaryar taron ministocin harkokin wajen kasashe mambobin kungiyar G20, da kuma taron Munich game da harkokin tsaro.
Ana dai fatan tattauna yadda za a aiwatar da shirin samun ci gaba mai dorewa na shekarar 2030, da batun kiyaye zaman lafiya, da inganta huldar abokantaka da kasashen Afirka, a yayin kwarya-kwaryar taron ministocin harkokin wajen kasashe mambobin kungiyar G20 na wannan karo. (Tasallah Yuan)