Rahotanni sun tabbatar da cewa an fidda kundin bayanai 50, ciki hadda wanda aka yiwa lakabi da "tsarin aiwatarwa na Hangzhou", da rahoton cibiyoyin hada hadar cinikayya na kasa da kasa, da ma na dabarun samar da ci gaba daga kasashe mambobin kungiyar.
Kundin tsarin aiwatarwa na Hangzhou, na kunshe da shawarwari da suka dace a bi, wajen karfafa ci gaban tattalin arzikin duniya, ta yadda zai zamo mai inganci da nagarta, ya kuma game daukkanin sassa. Kaza lika kundin ya kunshi yadda za a gudanar da manufofin kungiyar ta G20 cikin shekaru masu zuwa.
Hakan dai ya hada da dabarun raya tattalin arziki, da samar da ayyukan yi cikin gajeren lokaci, tare da hanyoyin kawo sauyi da ka iya daga matsayin samar da kayayyaki, da bunkasa zamantakewar al'ummun duniya a matsakaici da kuma dogon lokaci.
Sauran manufofin da taron ya amince da su domin tabbatar da ci gaban mambobin kungiyar ta G20, sun hada da dabarun wanzar da ci gaba a yayin da ake fuskantar yanayi na bazata, da na wanzar da ci gaba mai dorewa, tare da na kare muhallin halittu. (Saminu Hassan)