Ministan ya shaidawa manema labarai jiya Juma'a a Abuja cewa, manufar farfado da tafkin ita ce, rage tasirin sauyin yanayi a Nijeriya da sauran kasashe makwabtanta
Hukumar bunkasa ilimi, kimiyya da raya al'adu ta MDD UNESCO ta bayyana tasirin sauyin yanayi da karancin abinci da tsaro da gudun hijira da ayyukan ta'ddanci a matsayin matsalolin da yankin ke fuskanta.
A shekarun 1960, tafkin na da yankin kasa na kusan square KM dubu ashirin da biyar, amma ya ragu zuwa dubu biyu da dari biyar a shekarar 1985, daga baya kuma ya karu zuwa Square KM dubu hudu da dari shida da casa'in da takwas a shekarar 2013. (Fa'iza Mustapha)