in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masu bada tallafi za su taimakawa Nijeriya da yankin Tafkin Chadi da dala miliyan 672.
2017-02-25 12:55:29 cri
Masu bada tallafi na kasashen waje, yayin wani taron kan bada agajin jin kai da ya gudana jiya a birnin Olso na kasar Norway, sun yi alkawarin tallafawa arewa maso gabashin Nijeriya da yankin Tafkin Chadi da dala miliyan dari shida da saba'in da biyu.

Cikin wata sanarwa da Gwamnatin kasar Norway ta fitar, yayin taron masu bada gudunmuwa goma sha hudu, sun yi alkawarin bada dala miliyan dari hudu da hamsin da takwas ga ayyukan jin kai a bana, da kuma karin dala miliyan dari biyu da goma sha hudu da za a yi amfani da shi a badi.

MDD da hadin gwiwar Nijeriya da Jamus ne suka shirya taron da ya samu mahalarta kimanin dari da saba'in.

Za a tura kudin ga MDD da hukumar kula da 'yan cin rani ta duniya da kungiyar Red Cross da kuma kungiyoyin bada agaji na kasar Norway daban-daban dake aiki a kasashen da abun ya shafa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China