in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Aljeriya ta jaddada matsayinta game da warware matsalar Libiya ta hanyar siyasa
2016-11-20 12:43:03 cri

Kasar Aljeriya, ta bakin ministan harkokin yankin Magreb, kungiyar tarayyar Afrika da kungiyar kasashen Larabawa, mista Abdelkader Messahel, ya jaddada matsayinsa kan wata hanyar siyasa bisa tushen yin shawarwari domin warware rikicin Libiya. Yarjejeniyar siyasa ita ce muhimmiyar hanya mai karfi dake cikin hannun 'yan kasar Libiya a wannan muhimmin lokaci, in ji ministan Aljeriya bayan wata ganawa a ranar Asabar a birnin Alger tare da shugaban jam'iyyar El Taghyeer wato jam'iyyar kawo sauyi, kuma mamba na kwamitin sasanta 'yan kasar Libiya, mista Guma El-Gamaty. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China