Sin ta taimakawa kasar Zimbabwe wajen rage yawan mutane da suka kamu da ciwon sankarar mahaifa

A matsayin daya daga cikin ayyukan kiwon lafiyar mata da yara guda 100 a kasashe masu tasowa da kasar Sin take gudanar, an kaddama da aikin bada jinya ga mutanen da suka kamu da ciwon sankarar mahaifa da kasar Sin ta gudanar a asibitin Parirenyatwa dake birnin Harare na kasar Zimbabwe. Za dai a shafe makwani biyu ana aikin jinya, da mu'amalar fasahohi, da sauransu a fannin yaki da ciwon sankara a mahaifa.
A gun bikin kaddamar da aikin, Sin ta bada na'urorin kyauta ga asibitin Parirenyatwa, kayayyakin da darajarsu ta kai dala dubu 500, don samun nasarar jinya da magance ciwon sankarar mahaifa a kasar. (Zainab)